2023: Kwankwaso ya yi wani Jawabi kan Marawa wani Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa baya
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP), Sanata Rabi’u Kwankwaso, ya karyata rade-radin da ake yi na cewa zai barwa wani Ɗan takarar wata jam’iyyar kafin zaben 2023.
DAILY POST ta rahoto cewa ana ta rade-radin cewa tsohon Gwamnan Jihar Kano zai marawa Ɗan Takarar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ko kuma mai rike da tutar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu baya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ambaliyar Ruwa Ta Kashe Mutum 3, Tare Da Lalata Gidaje Sama Da 1, 000 A Bauchi
Amma da yake magana ta bakin mai magana da yawun yakin neman zabensa, Mista Ladipo Johnson, dan takarar jam’iyyar NNPP ya ce yana neman yin nasara.
A cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Legas ranar Lahadi, Johnson ya ce: “Kwankwaso na cikin yin takara kuma zai lashe zabe.”
A cewarsa, Kwankwaso yana da dukkan abin da ake bukata domin ya gaji Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a zaben shugaban kasa na 2023.
Ya ce, “Ban san yadda mutane ke kawo wadannan maganganu da hasashe ba. Kwankwaso ba zai iya ba kuma ba zai sauka ga kowane dan takara ba.
“Kwankwaso ba ya cikin yin siyasa don yin sulhu. Yana da kwazo, tarihin kwarewa da kuma kishin siyasar da zai kai Najeriya ga tudun mun tsira”.
A wani labarin kuma:Yadda ƴan Amotekun suka Harbe Ɗana, Suka Ce Ɗan Ƙungiyar Asiri ne – Uwa ta koka
Wata tsohuwa mai suna Amoke Eweje ta zargi hukumar Amotekun reshen jihar Ogun da harbe danta mai suna Ayodeji Eweje tare da sanya masa sunan dan daba.
Mahaifiyar da ke cikin rudani tana kuka ga gwamnatin jihar Ogun da ta taimaka ta ceto danta daya tilo mai suna Ayodeji daga hannun jami’an kungiyar Amotekun, wanda ta ce ta harbe shi a ranar 24 ga watan Mayu.