Mambobin jami’iyyar APC a Jahar Anambra sun yi kira ga Ministan Ƙwadago Chris Ngige daya fito cikin jerin masu neman takarar shugaban Ƙasa a shekarar 2023.
Akwai yiwuwar jam’iyya ta bada tikitin takara a shiyyar Kudu maso Gabas, kuma mazauna Jahar na son Ministan ya yi amfani da wannan damar.
Ƴan jam’iyyar sun bayyana ra’ayin su a gidan Ngige a ranar Lahadi.
KARANTA WANNAN LABARIN: CAN ta yabawa Rundunar Ƴan Sandan Jahar Kaduna bisa cafke ƴan bindiga guda 2
Ƙudirin buƙatar fitowa takarar shugaban Ƙasar shi tsohon Ɗan Majalisar Ƙaramar Hukumar Orumba ta Arewa Bar Okonkwo Okom ya bayyana shi, inda Kwamishinan Tarayya na Hukumar Raba dai-dai Dr Uche Ibeabuchi ya goyi baya.
A cewar Okom, Ngige ya taɓa zama Gwamna wanda ƙwazon sa, bazai taɓa mantewa ba ga Al’ummar Jahar.
A jawabinshi Ngige ya bayyana cewar yana sane da irin buƙatar magoya bayan Jam’iyyar, yana mai ƙara dacewa ya cancanta ya zama shugaban ƙasa.
Ya ƙara dacewa, yanayin siyasar ƙasar wanda yanzu lokaci ne na shiyyar Kudu maso Gabas ta fitar da shugaban Ƙasa, yana mai cewa shiyyar ba zata iya mai da shi ya zama shugaban ƙasa ba tare da goyon bayan sauran shiyyoyin ba.
Ngige ya yi kira ga mambobin jami’iyyar da su bashi lokaci zuwa bikin Easter domin duba yiwuwar bukatar su.
Comments 1