2023: Mambobin APC sun sauya sheƙa zuwa PDP a Sokoto
Kimanin mambobin jam’iyyar APC 1,868 a jihar Sokoto ne suka sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP gabanin babban zaben shekara mai zuwa.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin jam’iyyar PDP na jihar, Malam Hassan Sanyinnawal, ya fitar a Sokoto ranar Alhamis.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-yanzu: Buhari Yana Jagorantar Taron Majalissar Tsaro Ta Kasa
A cewar Sanyinnawal, ‘yan kasuwa ne daga al’ummomi 10 a fadin jihar, shugaban jam’iyyar PDP na jihar, Alhaji Bello Goronyo, ya tarbe su a Sokoto ranar Laraba.
Ya ruwaito Goronyo, wanda ya samu wakilcin shugaban jam’iyyar na shiyyar Sokoto ta tsakiya, Alhaji Muhammad Dangoggo, yana bada tabbacin sabbin masu shigowa jam’iyyar na daidaitawa da sauran ‘ya’yan jam’iyyar PDP.
Shugaban jam’iyyar PDP ya yi alkawarin daukar sabbin mambobin tare da yin kira gare su da su yi amfani da kwarewarsu a harkokin siyasa da kasuwanci don tabbatar da nasarar jam’iyyar a zaben 2023 mai zuwa.
Shima da yake jawabi, Ɗan Takarar gwamnan jihar a karkashin jam’iyyar PDP, Malam Sa’idu Umar, ya yi maraba da sabbin mambobin tare da yin alkawarin hada kai da dukkaninsu domin samun nasarar jam’iyyar.
Umar ya taya wadanda suka sauya sheka murna, yana mai cewa, “Shawarar da suka yanke ya nuna kishinsu na goyon bayan kyakkyawan salon shugabanci na Gwamna Aminu Tambuwal.”
Alhaji Lawali Lalala, wanda ya yi magana a madadin wadanda suka sauya shekar ya ce sun yanke hukuncin ne sakamakon samun su da laifin yunkurin ci gaban da gwamnatin PDP ke yi a jihar.
Lalala ya yi alkawarin ba jam’iyyar PDP cikakken biyayya da goyon bayansu tare da ba su tabbacin hada kai da shugabannin jam’iyyar domin ganin ta samu nasara a babban zabe mai zuwa.
A wani labarin kuma: Tsaro Mutane ke buƙata, ba kayayyakin Abinci ba — Bakare ga Gwamnatin Zamfara
Wani mai sharhi kan al’umma a jihar Zamfara, Alhaji Ahmed Bakare, ya koka kan yadda gwamnatin jihar ke ci gaba da raba kayan abinci da sauran kayayyakin masarufi a matsayin tallafin jin dadin jama’a ga ‘yan kasa masu karamin karfi ba zai kawo karshen ayyukan ‘yan fashi a jihar ba.
A wata hira ta musamman da ya yi da DAILY POST a Gusau, babban birnin jihar, Bakare ya ce kamata ya yi gwamnati ta mayar da hankali wajen tsara wata babbar dabara ta kawo karshen rashin tsaro.
Comments 1