Daga: Abbas Yakubu Yaura
Kimanin mambobin jam’iyyar PDP 616 ne suka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC a karamar hukumar Dukku a jihar Gombe a ranar Asabar din da muke shirin ban kwana da ita.
Wani tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Alhaji Kwairanga Dukku ne ya jagoranci sabbin masu sauya shekar da suka hada da shugabannin mata da matasa daga unguwanni daban-daban na karamar hukumar zuwa APC.
KARANTA WANNAN LABARIN: FG Ta Yi Barazanar Sanyawa Kamfanin CCECC Takunkumi Kan Gaza Aiwatar Da Ayyukan Jirgin Kasa
Dukku ya danganta matakin nasu da salon shugabanci nagari da manufa ta Gwamna Inuwa Yahaya.
Shi ma da yake nasa jawabin, Alhaji Bappah Maru, wanda tsohon mamba ne a kungiyar dattawan PDP, ya ce kokarin gwamnati mai ci a jihar wajen samar da ruwan sha a yankin ne ya sa shi ya koma APC.
Umaru ya ce matakin da suka dauka na komawa jam’iyyar APC shi ne don su yaba da manufofin da gwamnan ke da shi na inganta rayuwar al’umma.
Da yake maraba da sabbin mambobin, Gwamna Inuwa Yahaya ya ce gwamnatin jihar karkashin jam’iyyar APC ta kafa kyakkyawan shugabanci.
Yahaya wanda ya samu wakilcin kwamishinan kudi da ci gaban tattalin arziki, Alhaji Muhammad Magaji, ya ce yawan mutanen da suka shiga APC ya nuna babu wani fata ga jam’iyyun adawa a jihar a 2023, kamar yadda NAN ya ruwaito.
Gwamnan ya kara da cewa, “Tare da kwazon wadanda suka sauya sheka da aka samu a karamar hukumar Dukku, an kara karfafa jam’iyyar APC a Gombe, kuma hakan na nuna cewa damarmu a 2023 na kara haskakawa.
Mataimakin shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Dukku, Alhaji Yahya Kole, ya yabawa Yahaya bisa yadda yake gudanar da ayyukan sa na kawo sauyi a jihar.
Ya ce: “Wannan shi ya sa APC ta zama jam’iyyar da kowa ke rububin shiga kuma za mu ci gaba da karbar sabbin mambobi.”