By Abbas Yakubu Yaura
Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya sake jaddada cewa kasar ta fi samun rarrabuwar kawuna a karkashin jam’iyyar APC mai mulki, yana mai cewa “jam’iyyar ta yi rashin adalci a dukkan sassan kasar.”
Atiku ya bayyana haka ne a ranar Asabar a Abeokuta, jihar Ogun, yayin da yake jawabi ga wakilan jam’iyyar PDP gabanin zaben fidda gwani na shugaban kasa da za a yi.
Mataimaki Ga Shugaba Buhari Ya Ce Jibrin Kofa Har Yanzu Dan APC Ne
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a shekarar 2019, ya ce gwamnatin Olusegun Obasanjo, wadda ya yi aiki a matsayin mataimakin shugaban kasa daga shekarar 1999 zuwa shekarar 2007, ta hada kan ‘yan Nijeriya ta hanyar kafa gwamnatin hadin kan kasa.
Wazirin Adamawa ya ce ba zai yi sauki ba idan ba a samu hadin kai da zaman lafiya a tsakanin kabilu da addinai daban-daban ba, ya ce zai tabbatar da mika mulki ga jihohi da kananan hukumomi.
Sai dai ya yi alkawarin hada kan dukkan sassan kasar nan, ta hanyar bai wa kowane bangare ra’ayin nasa na kansa, da magance matsalar rashin tsaro da aiwatar da tsarinsa na bunkasa tattalin arzikin kasar domin kawo sauyi a kasar.
“Ba mu taba ganin irin rashin hadin kan da muke fama da shi a kasar nan ba, ko a lokacin yakin basasa; kuma me yasa muke samun rashin haɗin kai? Domin kuwa gwamnatin APC ba ta yi adalci a dukkan sassan kasar nan ba,” inji Atiku.
Yayin da yake alƙawarin haɗin kan Najeriya, ya tuna cewa “mun yi hakan a baya a shekarar 1999 lokacin da muka hau karagar mulki.”
Shima da yake magana, dan takarar gwamna a Ogun, Hon. Ladi Adebutu ta koka da matakin rashin tsaro da rashin aikin yi, inda ta bayyana kwarin gwiwar cewa jam’iyyar PDP “tana kan hanyar da za ta dawo da Najeriya da jihar Ogun zuwa ga nasara”.