Gamayyar kungiyoyi masu zaman kansu, da suka hardar da Sir Ahamadu Youths Council of Nigeria, da Arewa Youth Council and Arewa Youth Advocates For Good leadership sun bukaci jam’iyyun siyasa da su bi tsarin da ya dace na kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya na 2023, kada su tayar da rikici.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Kungiyoyin sun yi wannan kiran ne a ranar Laraba ta bakin shugabanninsu, Bilal Tijjani Paki, Zayyad Ayuba Alhaji da Ibrahim Munir Kankara, a wani taron manema labarai a Kano.
KU KARANTA KUMA Majalisar Dinkin Duniya Da Kanada Da NGO Sun Horas Da Matasa Harkar Siyasa
A cewar ƙungiyoyin sakamakon babban zaɓen ya nuna ainihin ra’ayin ‘yan Najeriya tare da yin kira ga matasan Najeriya da su daina amfani da wani ko wata jam’iyyar siyasa wajen kawo cikas ga zaman lafiya da haɗin kan ƙasar.
“Sakamakon zaben 2023 ya nuna muradin ‘yan Najeriya, kuma muna kira ga matasanmu da cewa kada sakamakon zaben ya zama sanadin rashin hadin kai da rigingimu a tsakaninmu. Babu wata maslaha ta kashin kai da ta wuce hadin kai da zaman lafiya a kasarmu.”
“Duk wani ko wata jam’iyyar siyasa da ke son kalubalantar sakamakon zaben, akwai hanyoyin da shari’a za ta bi don yin hakan, amma babu wani dan siyasa ko jam’iyyar siyasa da zai yi amfani da matasan mu don biyan bukatun kansa, ba za mu kyale shi ba, kuma ba za mu yarda ba.” kungiyar ta ce.
Sun kara da cewa zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya shi ne zaben da ya fi inganci da gaskiya da adalci a tarihin Najeriya.
“Mun kuma yaba da gaskiyar zaben 2023 da kuma kira ga dukkan ‘yan Najeriya su amince da tsarin.”
A Wani Labarin Kuma NJC Ta Dawo Da Alkalan Ekiti Da Aka Dakatar Shekaru 16 Da Suka Gabata
Majalisar shari’a ta kasa (NJC) ta mayar da mai shari’a Babajide Aladejana na babbar kotun jihar Ekiti aiki bayan shafe shekaru 16 da dakatar da shi.
An dakatar da Aladejana daga aiki a shekarar 2006 tare da tsohon babban alkalin jihar, Mai shari’a Kayode Bamisile, a karkashin gwamnatin tsohon alkalin alkalan Najeriya, Mai shari’a Alfa Belgore.