Daga: Abbas Yakubu Yaura
Shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP, Sanata Walid Jibrin, ya dage cewa jam’iyyar ba ta bangaranci bace, yana mai bayyana rashin adalci ga Arewa ta samar da dan takarar shugaban kasa da kuma shugaban Jam’iyyar na kasa.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, wanda shine dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar ya fito ne daga jihar Adamawa a arewa maso gabas, yayin da shugaban jam’iyyar na kasa, Iyorchia Ayu, ya fito daga jihar Benue dake arewa ta tsakiya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Matsalar Tsaro: Idan Na Sauka A Mulki, Mutanen Jihar Kogi Zasu Yi Kewa Na– Gwamna Bello
Sakamakon haka gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike da wasu masu ruwa da tsaki na jam’iyyar daga Kudancin kasar suka ci gaba da neman a tsige Ayu.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, Sanata Jibril ya ci gaba da cewa PDP ba za ta iya samar da shugaban kasa daga Arewa ba, shugaban jam’iyyar na kasa da kuma shugaban BoT duk daga Arewa ba.
“Har yanzu ina ci gaba da tsayawa kan wannan magana. PDP jam’iyya ce ta dimokuradiyya kuma ta kasa wacce ke kula da dukkan ‘yan Najeriya, ba ta bangaranci ba,” in ji shi.
Ya ce a matsayinsa na Shugaban BoT na jam’iyyar, dole ne ya fadi gaskiya, ba tare da la’akari da wanda gaskiyar za ta iya cutar da su ba.
A wani bangaren sanarwar ta ce “A matsayina na shugaban kungiyar BoT, ina da wa’adin shekaru 5, amma na shafe shekaru 4 da watanni shida, saura watanni shida kacal kamar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyyarmu ya tanada.
“Saboda haka, ba zan taba amincewa da duk wani zargi mara tsarki daga kowa ba. Zan ci gaba da zama a PDP har mutuwa ta.”
“Har yanzu ina ci gaba da cewa kungiyar ta BoT na matukar jiran rahoton kwamitin sulhu karkashin jagorancin gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Fintri da Farfesa Jerry Gana.”
“Bayan haka BoT za ta tattauna shi sosai tare da sanar da jama’a game da matakin da zai dauka na gaba.”
Ya kuma ba da tabbacin cewa, BoT za ta ci gaba da tattaunawa da duk wasu ‘yan jam’iyyar da suka ji haushi ciki har da na Jihohi da shiyyoyi.
Sanata Jibril ya bukaci jam’iyyar da ta mai da hankali sosai kan yadda za ta lashe dukkan mukamai a zaben 2023.
A wani labarin kuma Za Mu Yi Magana Da Yan ta’adda Da Yaren Da Suke Fahimta—-Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci jami’an tsaro da su farauto ‘yan ta’adda a cikin iyakokin Najeriya.
Buhari ya ce jami’an tsaro na da hurumin farauta, bibiyar su, da kuma magana da ‘yan ta’adda da yaren da suka fi fahimta.