2023: PDP Tace tana da tabbacin Lashe Jihar Lagos da wasu Jihohi 24
Jam’iyyar PDP ta sha alwashin lashe jihohi 25 ciki har da jihar Legas a babban zaben shekara mai zuwa.
Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Sanata Iyorchia Ayu, ya bayyana haka a wani taro a Abuja domin karbar rahoton kwamitin sulhu na jam’iyyar PDP na jihar Legas da Osun.
“PDP za ta samu gwamna a Legas da wasu mukamai da dama a majalisar dattawa, da wakilai, da na majalisu Dokoki na Jihohi,” in ji Ayu.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Tarayya za ta fara tallafawa Direbobi Mata domin karfafa sana’ar su
Ya kuma bukaci shugabannin jam’iyyar da ke da matsala da su warware irin wadannan matsalolin, inda ya ce idan aka yi hakan, jam’iyyar PDP za ta yi murna, kamar yadda na yi hasashe, akalla gwamnoni 25, sannan kuma za su samu babbar nasara a jam’iyyar.
A cewar Ayu, yayin da jam’iyyar a Legas ke cikin rudani, aikin da kwamitin da Cif Eyitayo Jegede ke jagoranta ya yi ya kara haskaka damar da PDP za ta samu a zaben badi.
Jegede, wanda shi ne dan takarar gwamna na jam’iyyar a zaben Ondo a 2022, ya shaida wa jigon na PDP cewa kwamitin ya warware duk wata matsala da ‘ya’yan jam’iyyar da suka ji haushi a jihohin Legas da Osun.
A wani labarin kuma: Dole ayi sulhu kan Adalci, Gaskiya da Dai-daito a PDP — Wike
Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Ezenwo Wike ya sake jaddada cewa Gwamnonin Jam’iyyar PDP G-5 dole ayi sulhu dasu kan gaskiya da adalci.
Gwamnan jihar Ribas ya bayyana hakan ne a wajen bikin kaddamar Gadar sama ta Rumuepirikom, karo na 8 da zuwa yanzu gwamnatin sa ta gina kuma ta kammala. Comrade Adams Oshiomhole, tsohon gwamnan jihar Edo ne ya kaddamar da aikin a ranar Laraba.