Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya mayar da martani ga kalaman gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai na cewa ya kamata ya mayar da hankali kan Nollywood maimakon tsayawa takarar shugaban kasa.
Tsohon Gwamnan Jihar Anambra ya ce zai yi aiki tukuru don inganta harkar Nollywood.
KARANTA WANNAN LABARIN: Masu Kada Kuri’a Sun Sha Alwashin Gurfanar Da INEC Gaban Kuliya Kan Wa’adin Karshe Na Karbar PVC
Obi ya bayar da amsar ne a ranar Lahadi yayin da ake nuna shirin Sunday Show a gidan talabijin na Arise.
Ku tuna cewa El-Rufai ya bayyana hakanne a lokacin da ake nunawa a shirin gidan Talabijin na Channels a cikin makon ya yi watsi da damar Obi a zaben shugaban kasa mai zuwa.
El-Rufai ya kuma yi ikirarin cewa Obi ba zai samu fiye da kashi 1% a Sokoto da kashi 2% a jihar Katsina ba.
Sai dai Obi ya ce zai mayar da hankali kan Nollywood idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa, yana mai kira ga ’yan wasan Najeriya da su mara masa baya tunda El-Rufai ya sanya shi a matsayin daya daga cikin su.
Ya ce, “Na gode wa El-Rufa’i da abin da ya ce, akalla ya ba ni wasu kaso; Zan yi aiki tuƙuru don inganta hakan. Masana’antar Nishaɗi na ɗaya daga cikin injunan da za su haɓaka mu a matsayinmu na Al’umma, zan mayar da hankali kan hakan da Nollywood.
“Kuma tun da ya ce ni dan wasan kwaikwayo ne, ina kira ga duk wadanda ke cikin masana’antar nishaɗi, ciki har da Nollywood, da su ba ni goyon baya.”
A wani labarin kuma, Shugaba Buhari Ya Yi Ta’aziyya Ga Iyalan ‘yan Banga 41 Da ‘Yan Ta’adda Suka Kashe
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a karshen mako ya yi tir da harin da aka kai wa ‘yan banga a dajin Yargoje da ke karamar hukumar Kankara a jihar Katsina, inda aka yi asarar rayuka da dama.
Jaridar DAILY POST ta rawaito cewa rundunar ‘yan sanda a jihar Katsina a ranar Juma’a ta tabbatar da mutuwar ‘yan kungiyar ‘yan banga ‘Yansakai su 41 a wani harin kwantan bauna da ‘yan ta’adda suka kai a dajin Yargoje.