By Abbas Yakubu Yaura
Jam’iyyar adawa ta PRP na kokarin hadewa da wasu kungiyoyin siyasa gabanin gudanar da babban zaben shugaban kasa na 2023 domin kawar da jam’iyyar APC mai mulki da babbar jam’iyyar adawa ta PDP.
Shugaban jam’iyyar na kasa Falalu Bello ne ya bayyana hakan ga manema labarai jim kadan bayan kammala taron kwamitin ayyuka na kasa da kwamitin amintattu da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a Abuja ranar Asabar.
Ya ce, “Muna duba gayyatar da aka yi masa na hada kai da kulla kawance. Muna tattaunawa da wasu kungiyoyi, wato NCFront misali, da kuma Rescue Nigeria Mission. Wannan yunkuri ne guda biyu da aka kirkira domin kafa babbar jam’iyya don kalubalantar mulkin PDP da APC a Najeriya.
“Yawancin wadannan jam’iyyu suna ganin ya zama dole mu kafa gwamnatin kasa a 2023.
Sai dai Wannan batu ya mamaye taron. Mun samu takarda daga Farfesa Attahiru Jega kan hadaka da kawance, wanda aka tattauna a kai; kuma mun amince da abin da za mu yi.”
Bello ya bayyana cewa jam’iyyar PRP za ta tsayar da dan takarar shugaban kasa a zaben 2023 daga ko’ina a fadin kasar nan.
“Ko mun shiga kawance ko hade, an warware wannan batu. Kowa daga ko’ina a Najeriya yana da ’yancin ya zo ya tsaya takarar shugabancin kasa a karkashin jam’iyyar PRP
“Abin da ke da muhimmanci a gare mu shi ne mutum mai aminci, ba don yana da wadata ko uban uba ko masu tallafa musu ba. Nan ba da jimawa ba zamu samar da tsarin shugabanci a Najeriya, kuma wannan samfurin zai shafi fadar shugaban kasa, gwamnoni, da ‘yan majalisar dokoki ta kasa,” inji shi.