2023: Tikitin Peter Obi/Baba-Ahmed Yafi kowane nagarta – Gamayyar Ƙungiyoyi
Gamayyar Ƙungiyoyin Farar Hula, Coalition for Good Governance (COG) sun amince da dan takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, a zaɓen 2023.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ma’aikacin Gwamnati Zai Maido Da Albashi Na Shekara 11 Akan Takardun Bogi
Gamayyar dai ta kunshi jam’iyyun siyasa 15 da aka soke rajista a kasar da kuma wasu tsoffin ƴan takarar shugaban kasa.
A cewar wata sanarwa mai dauke da sa Hannun Shugaban su na Ƙasa Engr. Okey Chikwendu da Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa, Don Anthony Harmattan, Ƙungiyar sun bayyana Obi da abokin takararsa, Yusuf Datti Baba-Ahmed a matsayin wanda ya fi kowa amincewa a tsakanin sauran ‘yan takara.
“Zabin ya ta’allaka ne kan tantance tikitin tare da ’yan takara masu sahihanci wadanda aka gwada, amana da kuma nuna isashen basira don ceto al’ummarmu daga halin da muka tsinci kanmu a ciki da kuma biyan bukatun al’ummar Nijeriya wanda yake daidai da adalci ba tare da la’akari da ƙabila ko ɓangaren ci.
“Saboda haka mun amince da sake canza ma ofisoshinmu suna a fadin kasar a matsayin ofisoshin yaƙin neman zaɓe. Tsarin mu a duk fadin Jihohi 36 da kananan hukumomi 774 za su goyi bayan tikitin Peter Obi/ Datti Baba-Ahmed karkashin jam’iyyar Labour,” in ji sanarwar.