Shugaban ƙungiyar Miyetti Allah Abdullahi Badejo ya bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Legas Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ba zai gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaɓen shekara ta 2023 ba.
Sannan Badejo ya ƙara da cewa abu ne mai wahalar gaske yankin Inyamurai su samu damar mulkar ƙasar nan.
Badejo ya ce bai yadda da tsarin yadda Kudancin kasar nan ke yin mulkinsu, duba da irin yadda suke nunawa ‘yan arewa tsangwama da ƙabilanci.
Kamar yadda ya bayyana “Ina da tabbacin Tinubu ba zai taɓa mulkar Najeriya ba, su kuwa yankin Inyamurai su ma ba zasu taba yin mulki ba, saboda idan suka Bahaushe a kudu sukan kirasa da ɗan kungiyar Boko Haram ko kuma wani suna na ɓatanci, shi yasa nace ba zasu mulki ba saboda suna da wani mugun abu a ransu”.
Da aka tambaye sa ko yana ganin shugaba Muhammadu Buhari zai iya samun nasara a zaɓen shekara ta 2015 ba tare da taimakon Tinubu sai yace “na fada maka zaɓen 2015 ya zama tarihi yanzu, kawai abinda na sani shi ne Tinubu ba zai taba tama shugaban kasa ba, saboda ya ya fi shugaba Muhammadu Buhari tsufa, kuma wasu suna kallonsa a matsayin jagoran Yarbawa, to, abun ba haka yake ba” cewar Badejo.