A yau ne Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC zai gana da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a Abeokuta, jihar Ogun, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.
Taron dai wani bangare ne na tuntubar da yake yi da kuma gyaran hanya domin tabbatar da takararsa ta shugaban kasa.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamna Dapo Abiodun, wato Kunle Somorin, ya ne ya sanar da hakan a safiyar Larabar nan.
Mohammed Salah Ya Bayar Da Kyautar Makudan Kudi Don Gyara Coci
“Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu zai ziyarci Abeokuta, jihar Ogun a yau, Laraba.
“Ya shirya ya ziyarci shugaban kasa Olusegun Obasanjo da karfe 10:00 na safe kuma ya yi jawabi ga mutane a filin wasa na MKO Abiola,” in ji Somorin a cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai.
Wata sanarwa da shugaban jam’iyyar APC na jihar, Yemi Sanusi ya sanya wa hannu ta ce “dukkan shugabannin jam’iyyar da mambobin, za su hallara cikin gaggawa.”
Wannan shine karo na uku da Tinubu zai kai ziyara jihar Ogun a kan takararsa ta shugaban kasa.
A cikin watan Fabrairu, ya gana da dukkan manyan sarakunan jihar, kuma ya sanar da su da burinsa.
A ranar 2 ga watan Yuni, Tinubu, gabanin zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar, ya gana da wakilan jam’iyyar APC a Abeokuta, inda ya bayyana irin rawar da suka taka wajen tabbatar da shugaba Buhari a 2015.
A ziyarar da ya kai a baya, Tinubu bai ziyarci Obasanjo ba, kamar yadda aka dage taron da aka shirya yi da tsohon shugaban kasar a watan Mayu.
An san Obasanjo da Tinubu abokan gaba ne na siyasa, wadanda tun zamaninsu na Shugaban kasa da Gwamnan Jihar Legas.
Amma a shekarar 2013, Tinubu ya jefar da hamayyar siyasa a bayansa lokacin da ya roki Obasanjo ya zama dan takarar jam’iyyar APC a zaben shugaban kasa na 2015.
Kuma bayan Buhari ya ci zabe, Obasanjo da Tinubu sun koma tafiya a yadda suka saba.
Ziyarar da tsohon Gwamnan Legas ya shirya a yau ita ce ta nuna goyon bayan Obasanjo ga takararsa ta shugaban kasa, kamar yadda wakilinmu ya fahimta.
Obasanjo wanda ya sha alwashin ba zai amince da duk wani dan takara cikin gaggawa ba, tun daga lokacin ya ajiye zabinsa a zabe mai zuwa kusa da kirjinsa.
Baya ga ganawa da Obasanjo, ana sa ran Tinubu zai yi jawabi ga ‘yan jam’iyyar APC a filin wasa na MKO Abiola da ke Kuto, Abeokuta.