By Abbas Yakubu Yaura
Tsohuwar kwamishiniyar ayyuka na musamman ta Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq, Hajiya Aisha Ahmad Pategi, ta yi kira ga al’ummar jihar Kwara ta Arewa da su yi watsi da duk wani dan asalin su da ya zabi jam’iyyar APC a 2023.
Aisha ta fice daga APC zuwa jam’iyyar adawa ta PDP a wani biki da aka gudanar a karamar hukumar Pategi ta jihar.
Tsohuwar mamba a majalisar ministoci, Aisha ta fara aiki a matsayin kwamishiniyar kananan hukumomi, masarautu da ci gaban al’umma a lokacin da ake zargin an karkatar da kudaden kananan hukumomi Naira miliyan 300 a jihar.
Da take magana a lokacin shirin, tsohuwar kwamishiniyar ta bayyana APC a jihar a matsayin “Majalisar tashin hankali ta Fugi” saboda “rikicin da ya ci gaba.”
Da take magana kan gogewarta a lokacin da take cikin majalisar ministocin ta, ta ce “Na yi kokarin tuntubar masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC a lokacin amma ko daya bai damu ba dani ba.”
Wannan dai bashine karon farko da ake samun sauya sheka ba daga wannan jam’iyyar zuwa waccan jam’iyyar biyo bayan kasuwar bukata irin ta siyasa.
Ko a ranar Talata 29 ga watan Maris sai da wani jigo a jam’iyyar ta PDP Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana ficewa daga jam’iyyar zuwa wata da ba’a bayyana ba a hukuman ce amma bisa wasu rahotanni da suke zaga yawa sun ce ya koma jam’iyyar NNPP
Kafin dai ficewar Kwankwaso daga jam’iyyar ta PDP sai da dan takarar gwamna a jihar ta kano Abba Gida Gida ya fice daga jam’iyyar zuwa ta mai gidan sa wanda suka ce sun fice daga jam’iyyar ne bisa wasu dalilai na rashin adalci.
Comments 1