Dan takarar gwamna a jam’iyyar NRM ta kasa reshen jihar Adamawa Alhaji Aliyu Maina ya rasu.
Olusola Afuye, Sakataren Yada Labarai na jam’iyyar taNRM ne ya tabbatar da mutuwar Maina.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Mutuwarsa na zuwa kasa da kwanaki 30 kafin babban zaben wata mai zuwa.
KARANTA HAKANAN Yar Takarar Shugaban Kasa A Jam’iyyar NRM Ta Bukaci Yan Najeriya Kada Su Zabi Rubabbun Yan Siyasa
An rahoto cewa ya rasu ne a ranar Laraba, 25 ga watan Janairu bayan gajeriyar jinya a Abuja, a ranar ne kuma aka tabbatar da rasuwar dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP a jihar Abia, Farfesa Uchenna Ikonne.
“A cewar sanarwar da ‘yan uwansa suka fitar, marigayi Alhaji Abba Maina ya rasu ne a ranar Laraba, 25 ga watan Janairu a gidansa da ke babban birnin tarayya Abuja, bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya.
“An binne shi kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. Muna rokon Allah Madaukakin Sarki ya jikansa ya baiwa iyalansa da dukkan masoyansa hakurin jure rashi,” inji Afuye.
Jaridar Daily Post ta rawaito cewa Yayin da yake kira ga ‘yan siyasa da ‘yan kasuwa da su nuna kulawa da soyayyar dangin marigayi Maina a lokacin zaman makoki, ya ce za a sanar da jama’a cikakkun bayanai game da shirye-shiryen bayan tattaunawa da iyalansa.
A Wani Labarin Kuma NLC Ta Bukaci CBN Ya Tsawaita Tare Da Sake Duba Manufofin Sabbin Kudin Naira
Kungiyar Kwadago ta Kasa NLC ta bukaci babban bankin Kasa CBN ya kara wa’adi daga ranar 31 ga watan Janairu domin kawar da tsofaffin takardun kudi da ake amfanj da su a kasar.
Mista Ayuba Wabba, shugaban kungiyar ta NLC, ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai ranar Alhamis a Abuja kan nasarorin da ya samu da kalubalen da ya fuskanta a matsayinsa na shugaban majalisar kungiuar na tsawon shekaru takwas.