2023: Wani Sarki a Ilori ya buƙaci Gwamna Abdulrazaq ya nemi wa’adi na biyu
Mai Martaba Sarkin Ilori kuma Shugaban Majalisar Sarakuna ta Jahar Kwara Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari a ranar Talata yace da Dukkanin zuciyar sa yana goyon bayan Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq ya nemi wa’adi na biyu a matsayin Gwamnan Jahar Kwara.
KARANTA WANNAN LABARIN: Hadimin Wani Gwamna ya gargaɗi Matasa dasu kula da Abokanan da suke tarayya dasu
Sulu-Gambari ya bayyana cewar Abdulrazaq ya yi Kyakkyawan aiki da namijin ƙoƙarin daya kamata ya samu dama ta biyu domin kammala ayyukan sa.
Basaraken ya bayyana haka a lokacin da yakai ziyarar Sallah ga Gwamnan a gidan Gwamnatin Jahar dake Ilori da aka fi sani da “Bereke”, a matsayin wani aikace-aikace na Shagulgulan Bikin Sallah.
“Gwamna ya kasance yana aikin daya kamata. A taƙaice shine mutumen daya fi dacewa. Ina mai farin cikin faɗin cewa ina Son Gwamna ya nemi wa’adi na biyu na mulki,” inji shi.
Sulu-Gambari wanda ya bayyana cewar Abdulrazaq yana da iko da damar da zai nemi wa’adi na biyu kamar yadda Kundin Tsarin Mulkin ya ayyana, “wannan dama ce da kowane ɗan ƙasa cewa idan mutum yayi wa’adin farko, to zai iya neman wa’adi na biyu.
Sarkin yayi addu’a ga Allah daya Cigaba da Jagoranci ga Gwamnan domin ya cigaba da aikata Kyakkyawan aikin daya kasance yana yi a faɗin Jahar.
A jawabin shi, Abdulrazaq ta bayyana ziyarar Sarkin a gidan Gwamnati a matsayin wani manuniya na Kyakkyawar dangantaka dake tsakanin Sarakuna da Gwamnatin Jahar.
Comments 1