Wata Ƙungiya mai rajin ganin an zaɓi Bukola Saraki a matsayin Shugaban Ƙasa tayi kira ga masu ruwa da tsaki a Jahar Gombe musamman a Jam’iyyar PDP dasu goyi bayan takarar Tsohon Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya.
Dayake jawabi jim kaɗan bayan yayi taron Shuwagabanni a Sakatariyar Jam’iyar PDP na Ƙasa a ranar Talata, Shugaban ta Farfesa Iyorwuese Hagher ya bayyana cewar tsohon Gwamnan Jahar Kwara shine amsar maganin matsalolin dake fuskantar Ƙasar.
KARANTA WANNAN LABARIN: 2023: Kuyi Zaɓe da Hankalin ku, ba Cikin ku ba — Gbenga ya gargaɗi ƴan Najeriya
A cewar sa, Ƙasar ta Kasance tana yin baya tun lokacin da Jam’iyyar APC ta Karɓi mulki, yana mai jaddada cewa Najeriya na cikin wani mawuyacin hali a tarihin ta.
Hagher “mun zo Gombe domin wayar wa Al’umma kai, da kuma cusawa mutane son Ƙasar nan. Munje Jahohi da dama, kuma zamu je dukkanin Jahohin Kasar nan, kafin Bukola Saraki ya fito ya nuna ra’ayin sa na ƙudirirrikan su.
Ya bayyana cewar Saraki ya nuna kyakkyawan Shugabanci a matsayin sa na tsohon Shugaban Ƙungiyar Gwamnoni, yana mai cewa yayi ƙoƙari wajen haɗa kan ƙasar nan.
Comments 1