2023: Wike zai yiwa Tinubu aiki domin yaci Zaɓen Shugaban Ƙasa – Masari
Gabanin Zaɓen shugaban kasa a Najeriya mai zuwa, Ibrahim Masari, tsohon abokin Takarar Bola Ahmed Tinubu Ɗan Takarar jam’iyyar All Progressives Congress,APC, ya yi tsokaci kan Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas, inda yace yana yi wa jam’iyyar aiki.
Masari ya shaidawa Sashen Hausa na BBC a ranar Laraba cewa Wike zai yi aiki don ganin Tinubu ya zama Shugaban Ƙasa
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamna Abdulrazaq ya koka kan yawaitar ta’addanci a Jihar
“Ganawar da suka yi, ta kasance kan zaben shugaban kasa na 2023 kuma da yardar Allah za mu yi aiki tare da mai girma Gwamna Nyesom Wike.
“Zai taimaka kuma zamu ci zabe cikin sauki, da yardar Allah,” in ji Masari.
Hakan na zuwa ne lokacin da rahotanni suka ce Tinubu ya gana da wasu gwamnonin jam’iyyar PDP, ciki har da Wike a Landan.
DAILY POST ta tattaro cewa Wike da wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP ciki har da Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwe sun tafi kasar Ingila domin yin wata muhimmiyar ganawa.
Ku tuna cewa Wike ya yi takun-saka da jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP, dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar, tun bayan zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar.
Wike ya ji takaicin yadda Atiku ya yi biris da shi wajen zaben abokin takararsa.
Atiku dai ya zabi Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta ne a matsayin abokin takararsa, sabanin shawarwarin ‘yan PDP.