2023: Ya kamata INEC ta haramtawa Ƴan Takarar da ke ziyartar coci-coci da masallatai – Adeyanju
Wani mai fada a ji a shafukan sada zumunta, Deji Adeyanju, ya bukaci Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta kasa (INEC) ta haramtawa ‘yan takarar da ke ziyartar coci-coci ko masallatai domin neman goyon baya gabanin babban zaben 2023.
KARANTA WANNAN LABARIN: Nagartar Malam Shekarau Ce Tasa Muke Da Tabbaci Akansa A PDP – Makarfi
Jaridar DAILY POST ta rawaito cewa daga majami’u zuwa masallatai har ma da wuraren ibada, ana ganin wasu ‘yan takara na tafiya daga wannan wuri zuwa wani wuri suna neman ƙuri’u.
Amma, Adeyanju a wani sako da ya wallafa a ranar Talata, ya ce dokar Najeriya ta hana amfani da addini ko kabilanci wajen yakin neman zabe.
Ya ce: “2023: Ya kamata INEC ta haramtawa ‘yan takarar da ke zuwa coci coci ko masallatai yakin neman zabe ko neman goyon bayan kuri’a. Dokokinmu sun hana amfani da addini ko kabilanci wajen yakin neman zabe.”
Tun da farko Adeyanju ya shawarci dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, da ya fara gina gine-gine maimakon zuwa coci-coci kamar mai neman zama shugaban CAN.
A safiyar ranar Talata, ya caccaki mataimakiyar dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Legas, Funke Akindele, da cewa tana hidimar coci.
“Kallon bidiyon Funke Akindele, mataimakiyar dan takarar gwamna a PDP na yakin neman zabe, yin ibada a cocin Legas abin ban dariya ne. Ta kusa fita hayyacinta a cikin haka. ‘Yan siyasa su nisantar da siyasar su daga coci,” Adeyanju ya wallafa a Facebook