Tawagar wasu Dattawa daga Daura garin su shugaban kasa Muhammadu Buhari a jihar Katsina, sun yabawa gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello dangane da irin goyon bayan da yake baiwa shugaban kasa a ko da yaushe.

Tawagar wadda ta ƙunshi masu rike da Sarautun gargajiya da kuma masu ruwa da tsaki a harkar siyasar jihar waɗanda suka fito daga kafatanin ƙananan Hukumomin Katsina sun yi wannan yabon ne lokacin da suka kaiwa gwamna Bello ziyara a ranar Alhamis.
Da suke magana ta bakin mai magana da yawun su Injiniya Mato Daura, ya yaba da irin goyon bayan da gwamnan yake baiwa shugaban Kasa a koda yaushe, domin ganin shugaba Buhari ya samu kaiwa ga ci.
DUBA WANNAN LABARIN: Badaƙala: Gwamna Zulum Yayi ziyarar bazata wasu cibiyoyin kula da lafiya
Mato ya kuma bukaci Gwamna Bello da ya ajiye komai a gefe tare da tsayawa takarar shugabancin kasa a zaben shekarar 2023 dake tafe.
Da yake nasa jawabin, gwamnan jihar Yahaya Bello ya godewa tawagar dattawan, bisa ziyarar da suka kai masa, yana mai cewa ayyukan raya kasa da shugaba Buhari ke shimfidawa a Najeriya, ba wanda zai kushe sai mutum kawai.
Comments 1