Kwamitin wanzar da zaman lafiya na kasa (NPC) ya tsara ranar Alhamis mai zuwa ga ‘yan takarar shugaban kasa da su rattaba hannu kan yarjejeniyar ‘yanci, gaskiya da lumana, gabanin yakin neman zabe.
A watan Janairu, za su kuma rattaba hannu kan yarjejeniyar amincewa da sakamakon zaben na 2023.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Shugaban kwamatin, Janar Abdulsalami Abubakar, ya bayyanawa manema labarai bayan taron kwamitin tare da hadin gwiwar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da aka gudanar a garin Minna na jihar Neja a ranar Alhamis din nan. Ya bukaci ‘yan Najeriya da su daina sayar da kuri’unsu a lokacin zabe.
KARANTA KUMA: Yan Takarar Shugaban Kasa Na Yankin Kudu Suna Ganawar Sirri
A cewarsa, a wannan lokaci na zabe, ‘yan takarar shugaban kasa za su rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya guda biyu. Sun ƙunshi rattaba hannu kan yarjejeniya don karɓar sakamakon zabe da kuma tabbatar da yaƙin neman zaɓe na gaskiya ba tare da nuna bambanci ba.
A nasa jawabin, Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmud Yakubu ya yaba da irin jarumtakar matakai da shigar kwamitin NPC wajen ganin an gudanar da zabukan 2023 cikin kwanciyar hankali.
Ya bayyana cewa hukumar ta shirya gudanar da zaben ne gabanin dage takunkumin yakin neman zabe.
Shugaban na INEC ya lura cewa an aiwatar da ayyuka 8 cikin 14 da aka tsara, ya kuma bukaci kafafen yada labarai da su tabbatar da cewa jam’iyyu da ‘yan takara sun mayar da hankali kan yakin neman zabe.
Tashar talabijin ta Channels ta rawaito cewa, Taron ya samu halartar mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar; Archbishop Hassan Mathew Kuka, tsohon HOS, Yayale Ahmed da sauransu.
A wani labarin kuma: Osinbajo Na Son Karin Mata Masu Matsayi A Shugabanci
Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya ce samun daidaito da adalci, wakilcin mata da shiga harkokin siyasa da gwamnati zai yi babban tasiri ga makomar zamantakewar tattalin arzikin kasa da kuma ci gaban kasa baki daya kamar misalin ilimin ‘ya mace.
Farfesa Osinbajo ya bayyana haka ranar Alhamis a matsayin babban bako na musamman a taron shugabanni mata na 2022.