Wani Lauya Mai Kare Haƙƙin Bil’adama Festus Ogun yayi kira ga Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da yayi gaggawar korar Gwmanan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele.
Lauyan yayi wannan kiran a lokacin da yake maida jawabi akan rahoton dake yawo cewa Masoyan Emefiele sun sayi Tikitin Tsayawa Takarar Shugaban Ƙasa domin neman kujerar a Shekarar 2023.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gasar Zakarun Turai: Babu wata magana da za ta iya rage radadin Man City, Guardiola
Haɗakar Ƙungiyar data Ƙunshi Ƙungiyoyin Manoma Shinkafa da Ƙungiyoyin dake goyon bayan sa, gami da Abokanan Emefiele a ranar Juma’a suka sayi Tikitin Tsayawa Takarar gareshi.
Gwamnan Babban bankin ya musanta nuna ra’ayi a gareshi na neman Kujerar Shugaban Ƙasa, amma har yanzu yaƙi yin magana akan karɓar Tikitin.
Lauyan ya bayyana tsoron cewa yanzu Baitin Malin Najeriya, baya Lafiya lau a hannun Emefiele.
Yace “Gwamnan CBN Godwin Emefiele ya sayi Tikitin Tsayawa Takarar Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar APC akan Naira Miliyan 100. Wannan ya saɓawa Doka, da kuma lalata abinda ke cikin Bankin.
“Sashe na 9 na Dokar Babban Bankin Najeriya, Doka ta 2007, ta bada cewa Dukkanin Gwamnoni da Mataimakan su, dole su maida hankali wajen yiwa Al’umma aiki, kuma a lokacin da suke mulkin wuraren, dole zasu guji yin wani aiki na wucin gadi.