Daga: Abbas Yakubu Yaura
Tsohon sakataren yada labaran jam’iyyar PDP na kasa, kuma kakakin kungiyar dattawan Akwa Ibom, Sanata Anietie Okon ya ce duk wani yunkuri na jam’iyyar ko dan takarar shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar na yin watsi da Gwamna Nyesom Wike zai haifar da hadari.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta ta rahoto cewa har yanzu Gwamnan Jihar Ribas da magoya bayan sa na cikin fushi kan sakamakon zaben fidda gwani na shugaban kasa.
KARANTA WANNAN LABARIN: https://dimokuradiyya.com.ng/zabin-shettima-da-tinubu-yayi-tabbas-shine-hanyar-samun-nasarar-jamiyyar-apc-ganduje/
Lamarin ya kara ta’azzara ne bayan da Atiku ya zabi Gwamnan Jihar Delta, Ifeanyi Okowa a matsayin abokin takararsa da Wike wanda kwamitin wucin gadi da aka kafa don haka ya bayar da shawarar.
A halin da ake ciki dai akwai yunkurin gwamnonin jam’iyyar APC na neman Wike ya koma jam’iyyar amma har yanzu yunkurin bai samu sakamako mai kyau ba.
Sai dai Sanata Okon, wanda jigo ne a jam’iyyar PDP a jihar Akwa Ibom, a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a Uyo, a karshen mako, ya gargadi jam’iyyar PDP kan yin watsi da Wike.
Ya ce “irin wannan zai haifar wa jam’iyyar halaka domin Wike ya kasance ginshiki mai karfi a jam’iyyar.”
Ya ce, “Gwamnan Rivers, Nyesom Wike ya kasance dan takara mai karfi a jam’iyyar. Ya yi wa PDP yawa kuma ya ci gaba da kasancewa amintacce a jam’iyya.”
“Don haka tunanin yin watsi da shi tamkar yanke hukuncin kisa ne, ba wai bayan kwamitin da jam’iyyar ta kafa ta zabe shi da karfi ba.”
“Don haka zan ba Alh. Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP wanda na taya shi murna shawara, ya yi duk mai yiwuwa don tafiyar da lamarin cikin ruwan sanyi domin zaben shugaban kasa na 2023.”