Jam’iyyar PDP a jihar Nasarawa ta sha alwashin tura gwamna Abdullahi Sule zuwa kasar Saudiyya a shekarar 2023 dake tafe.
Mista Francis Orogu, shugaban jam’iyyar PDP na jihar ne ya bayyana haka a wata tattaunawa da manema labarai a karamar hukumar Karu a ranar Alhamis.
KARANTA WANNAN LABARIN: DSS Ta Janye Karar Da Take Yiwa Tsohon Mai Sasantawa Da ‘Yan Ta’adda, Tukur Mamu
Orogu ya yi zargin cewa gwamnan ya nuna cewa ba shi da ikon gudanar da mulkin jihar inda ya yi takama da cewa PDP za ta kore shi zuwa kasar Saudiyya a karshen wa’adinsa na farko.
Kalaman sa: “APC bisa ga dukkan alamu ta gaza wa al’ummarmu, saboda haka zabe mai zuwa na tafiya ne kawai ga PDP. Nan da 2023, za mu mayar da shi zuwa kasar Saudiyya.”
Mista Orogu ya caccaki gwamnan bisa zarginsa da shan alwashin murkushe duk wanda ya tsaya tsakaninsa da kujerar gwamna gabanin zaben 2023, yana mai tabbatar da cewa PDP ba za ta ji tsoro ba.
Sai dai ya yi gargadin cewa jam’iyyar adawa za ta bijirewa duk wata tursasawa da ake zargin jam’iyya mai mulki ta yi ta hanyar da ta dace, yayin da ya bukaci al’umma da su tabbatar sun kirga kuri’u.
Tun da farko, dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP, Dr David Ombugadu, ya yi kira ga shugabannin da su guji tayar da fitina.
Ya ce jam’iyyar PDP ba za ta gangara zuwa APC ba, yana mai cewa jam’iyyar za ta tsaya kan yadda za ta ciyar da kasar nan da jihar gaba.
A wani labarin kuma, Wata Mata Ta Gurfana Gaban Kotu Kan Zargin Wallafa Kayan Batsa Ga Wasu Ma’aurata A TikTok
Wata mata ‘yar shekara 34 mai suna Gift Okpomini, a ranar Alhamis ta tsaya a gaban wata kotun majistare da ke Ikorodu a jihar Legas, bisa zarginta da saka kayan batsa a kan wasu ma’aurata a shafin sada zumunta na Tiktok.
‘Yan sandan sun tuhumi Ms Okpomini, wadda ba a bayar da adireshinta ba, da laifuka uku da suka shafi halayya da ka iya haifar da ruguza amana, aika abubuwa masu hadari ko batsa ta hanyar rubutu da sata.
Sai dai kuma wanda ake tuhumar ta musanta zargin aikata Laifukan.