Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya a ranar Litinin, tace zata tattara tare da wayar da kan masu kaɗa ƙuri’a, gabanin Babban zaɓe na Shekarar 2023 domin gano waɗanda zasu zama Shuwagabanni a Ƙasar.
Shugaban Ƙungiyar reshen Jahar Lagos Rt. Rabaran Stephen Adegbite ya bayyana haka a tattaunawar shi da Kamfanin Dillancin Labaru na Najeriya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wani Uba yaci zarafin ɗiyan sa guda 3 a Lagos
Yace ilmantar da masu kaɗa ƙuri’a ya zama dole domin inganta harkokin siyasa, yana mai nuni dacewar zai inganta zaman lafiya, da lumana da inganta tattalin arziki a Ƙasar.
Adegbite wanda ya koka akan yawaitar shan wahalhalu da ake yi a Kasar, da rashin tsaro, yace wannan lamari ya faru ne saboda rashin nagartattun Shuwagabanni.
Yace Ƙungiyar CAN a matsayin ɗaya daga cikin masu faɗa aji ga Al’umma, ta fara tattara masu kaɗa ƙuri’a a rajistar katin ɗan ƙasa da ake yi gabanin Babban zaɓe.