Allah ya yi wa tsohon shugaban hafsan soji Nigeria Janar Mohammed Inuwa Wushishi rasuwa.
A cewar wata majiya mai tushe, Janar Wushishi ya rasu ne a wani asibitin Landan.
An haifi Janar Wushishi a shekarar 1940 a Wushishi hedikwatar karamar hukumar Wushishi ta jihar Neja.
Ya rike mukamin babban hafsan soji tsakanin Oktoba 1981 zuwa Oktoba 1983, a lokacin jamhuriya ta biyu.
Ya yi aikin sojan Nijeriya a wurare daban-daban, ciki har da Janar Hafsan Soja, 4 Infantry Division, Nigerian Army, 1976; Kwamanda, Kwalejin horas da jami’an soji dake garin Jaji na jihar Kaduna a Disamba 1979.