Shuhaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kafa wani sabon tarihi na kasancewa zababben shugaban kasa da bai yi jawabin ranar rantsuwa ba. Shugaban kasar tare da mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo, sun bar muhallin taron bikin rantsuwar ne bayan karbar rantsuwar da misalin karfe 10 na safe zuwa 11 a filin taron ‘Eagle skuare’ da ke Abuja. Tun bayan rantsar da Firai minista Sa Abubakar Tafawa Balewa, ya zama wata zaunanniyar al’ada ga duk sabon shugaban kasa na yin jawabi ga ‘yan kasa a ranar rantsarwa tare da fadar sabbin tsare-tsaren sa ga al’umma. Tafawa Balewa ya fara gabatar da irin wannan jawabin nasa a 1 ga Oktoba, a cikin jawabin nasa, ya jinjina wa ‘yan Najeriya bisa jajircewarsu na tsawon shekaru 60 na mulkin mallaka daga Turawan yamma. Haka shi ma, zababben shugaban Najeriya na biyu, Alhaji Shehu Shagari, ya gabatar da jawabi a ranar rantsar da shi 1 ga Oktoba 1983, inda a ciki ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su hada kai ba tare da la’akari da bambancin siyasa ba da kuma ganin cewa sojoji ba su sake karbar mulki ba. Olesegun Obasanjo, wanda ya zama shugaban kasa a jamhuriya ta Hudu a 29 ga Mayu, 1999, bayan kifar da gwamnatin Shagari da Buhari ya yi, cikin jawabinsa, ya yi barazanar cewa, ba wani da za a daga wa kafa kan kokarin yaki da cin hanci. Haka ma a shekarar 2003 bayan sake cin zabe, ya gudanar da jawabin rantsuwa. A jawabinsa kuwa a 2007 bayan zama shugaban kasa, Umaru Musa Yar’adua ya yi alkawarin kawo gyara a tsarin gudanar da zabe bayan da ya tabbatar da cewa an yi murdiya a zaben da ya kawo shi kan karagar mulki. Goodluck Jonathan ma, bayan zama shugaban kasa a 6 ga Mayu 2010 bayan mutuwar Yar’Adua, ya gabatar da jawabi, inda ya yi alkawarin dorawa kan inda tsohon maigidansa ya tsaya, wato Marigayi Yar’adua. Kuma a 2011 lokacin da ya sake lashe zabe ya yi kira ga ‘yan Najeriya kan hadin kan kasa. A lokacin jawabinsa na 29 ga Mayu 2015, bayan lashe zabe, Shugaban kasa Buhari ya gudanar da jawabi a wurin taron bukin rantsarwa, inda ya gabatar da shararren jawabin nan nasa a cikin harshen Turanci na “I belong to eberybody and I belong to nobody”, wato ‘Ni na kowa ne kuma ni ba na kowa ba ne’. To sai dai, wani abu, a wannan karon, bayan rantsar da shi tare da zagayen duba rundunar sojoji, bai yi wata ba sai shiga jerin gwanon motocinsa ya fice daga wurin, ba tare da gabatar da jawabin ba.