Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Jami’o’i ta kasa (JAMB) ta dage fara rajistan jarrabawar shekarar 2022/23.
Tun da fari dai an shirya fara yin rijistar ne a ranar Asabar 12 zuwa 19 ga watan Maris din shekarar 2022, amma hukumar JAMB ta mayar da fara rajistan jarabawa ranar 19 ga watan Maris zuwa 26 ga Maris, 2022.
Shugaban sashen hulda da jama’a na hukumar , Dr Fabian Benjamin a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata ya ce an dauki matakin ne don samun damar inganta dukkannin tsare-tsare ta hanyar da Dalibai zasu yi rijistan cikin sauki.
Ya ce ana sa ran kammala shirye shiryen cikin mako guda, Kuma kofa a bude take ga masu bada sha’warwari ta kowace fuska.
Yayin da yake bayyana cewa hukumar a shirye take ta gudar da ayyukanta cikin yanayi Mai kyau ga ‘yan Najeriya, ya ce za a fitar da sabbin tsare-tsare da ingantattun hanyoyin yin rijistar jarabawar ta UTME na shekarar 2022/23 ta hanyar shafin yanar gizon hukumar.
A cewarsa “Ya kamata Dalibai su bi tsarin rajistar kamar yadda hukumar za ta bayyana nan gaba.
Comments 1