By Abbas Yakubu Yaura
Wata kotun majistare dake zamanta a Akure, babban birnin jihar Ondo, ta yanke wa wata mata ‘yar shekara 36, Misis Opeyemi Omoyemi, hukuncin daurin shekaru hudu da rabi a gidan yari, bisa samun ta da laifin yiwa wani yaro Joel Sunday mai shekaru 12 munanan raunuka, wanda ya kasance dan aikin gidan tane.
Omoyemi, wata bazawara ta gurfana a gaban wata kotun majistare kan tuhume-tuhume biyar da suka hada da yunkurin kisan kai, cin zarafin yaro, cin zarafin mutane da dai sauransu.
An ce wacce ake zargin ta yi amfani da sanda da reza wajen raunata da dama a jikin mai taimakon aikin gidan wanda ta zarga da satar nama a cikin tukunyar miya.
Da yake yanke hukuncin, Alkalin Kotun Mai shari’a Olufunumilayo Edwin ya yanke wa wanda ake kara hukuncin daurin shekaru uku da rabi a kan tuhume-tuhumen farko na mugunyar cutar da ta yi wa wanda lamarin ya shafa a faifan bidiyon.
Kafin babban alkalin kotun ya yanke hukuncin, lauyan wanda ake kara, Foluso Kayode ya bukaci kotun da ta yi wa wanda yake karewa sassauci.
Ya kara da cewa wanda yake karewa, ita ce mai laifi na farko, ba a kama ta ba da wata dabi’a ta rashin mutunci