By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi ta kama wasu mutane hudu da ake zargi da aikata laifin fyade da kuma cutar da kananan yara a jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, PPRO, SP Nafi’u Abubakar, ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Birnin Kebbi ranar Alhamis.
Ya ce daya daga cikin wadanda ake zargin – Isah Wakili, da karfin tsiya ya yiwa wata yarinya ‘yar shekara 14 fyade a gidan aurensa.
“Wakil, dan shekara 25 a kauyen Tsohuwar Guguwa,dake karamar hukumar Ngaski ta jihar a ranar 21 ga watan Disambar shekarar 2021, da misalin karfe 11:00 na safe, ya yi lalata da wata yarinya ‘yar shekara 14 da karfin tsiya a wannan adireshin a cikin dakin aurensa.
“Wanda ake zargin ya aikata laifin ne lokacin da yarinyar ‘yar shekara 14 iyayenta suka aike ta zuwa gidansa domin ta karbo wata kwantena.
“Da samun rahoton, sai tawagar ‘yan sanda suka garzaya wurin da lamarin ya faru, suka kama wanda ake zargin.
“An gurfanar da wanda ake zargin zuwa kotu domin tuhumar sa da laifin aikata fyade,” in ji shi.
Mista Abubakar ya kuma ce an kama wani mai suna Ibrahim Musa a garin Gwandu da laifin yiwa wata yarinya ‘yar shekara 10 fyade.
“A ranar 7 ga watan Maris, da misalin karfe 9:00 na dare, wani Ibrahim Musa, mai shekaru 39 a garin Gwandu, da karfin tsiya ya yiwa wata yarinya ‘yar shekara 10 fyade mai adireshin daya, a cikin dakin dan uwanta.
“Wanda ake zargin ya aikata laifin ne a lokacin da yarinyar ta shiga ba wa dan uwanta abinci, wanda ba ya kusa.
“An kama wanda ake zargin kuma an gurfanar da shi gaban kotu domin tuhumar sa da laifin aikata fyade,” in ji shi.
PPRO ya ce ‘yan sandan sun kuma kama wasu mutane biyu da ake zargi da aikata fyade, wadanda suka yaudari wata yarinya ‘yar shekara 12 a cikin tanti tare da yi mata fyade.
“A ranar 24 ga watan Maris, da misalin karfe 10:00 na safe, wasu da ake zargin da yiwa wata yarinya fyade sun hada da Nura Bello,mai shekaru ‘30’ da Abdullahi Garba ‘25’ sun hada baki tare da yiwa wata yarinya ‘yar shekara 12 mai adireshin daya fyade a cikin tanti a gonar barkonon su da karfi.
“Bayan samun labarin an tattara ‘yan sanda kuma sun yi nasarar cafke wadanda ake zargin.
“An gurfanar da su a gaban kotu domin girbar abinda suka shuka,” in ji shi.
Ya shawarci al’ummar jihar da su yi taka tsantsan tare da baiwa ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro bayanai kan lokaci da za su taimaka wajen dakile miyagun laifuka.
NAN
Comments 1