By Abbas Yakubu Yaura
An kama wasu mutane 8 a unguwar Olowo da ke yankin karamar hukumar Odigbo a jihar Ondo, bisa zargin fasa bututun mai da ayyukan tace gurbataccen mai ba bisa ka’ida ba.
Jami’an hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya NSCDC ne suka cafke wadanda ake zargin a jihar.
Jaridar Dimokuradiyya ta tattaro cewa wanda ake zargin yana hulda da gurbataccen man fetur tare da gudanar da ayyukan fasa bututun man fetur da kuma ajiye shi ba bisa ka’ida ba.
Babban kwamandan hukumar leken asiri na musamman ne ya kama su wanda ya yi aiki da ingantaccen Rahotannin sirri.
Majiyoyi sun ce an kama su ne a maboyar su da misalin karfe 09:00 na ranar 21 ga watan Afrilu, 2022.
Kakakin hukumar na jihar, Daniel Aidamenbor ya tabbatar da kama mutanen takwas din.
Aidamenbor ya ce an kama mutane takwas a wurin da lamarin ya faru kuma suna loda kayayyakin da ake zargin gurbatattun kayayyaki ne a cikin shagon.
“Bakar Toyota Sequoia mai lamba Legas APP 134 DX dauke da keg 70 na Lita 25 na gurbataccen AGO.
“Kegs 28 mai cin lita 25 kowanne na gurbataccen AGO wanda suke dauke dasu daga wurin da lamarin ya faru, injinan fanfo guda shida da injin kirga kudi guda daya.
“Haka nan a wurin da aka rufe tare da tsare su, an kuma kwato abubuwa kamar haka, lita 25 na 19keg na gurbataccen man fetur AGO, ganguna 5 masu daukar lita 200 na AGO, ganguna 2 mai cin lita 200 wanda ya cika da kuma rabin ganguna 2 na lita 200.
“Sauran tankunan ajiya guda biyu ne dauke da lita 3500 na gurbataccen man fetur, An kuma gano tankunan ajiya na karkashin kasa mai dakuna hudu a wurin da lamarin ya faru.
“Kashi na farko babu komai a ciki, na biyu kuma yana dauke da lita 2,800, na uku kuma yana dauke da lita 1,500, shi kuma na hudu yana da lita 16,500 na gurbataccen iskar gas na AGO.
Aidamenbor ya ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a kotu a karshen binciken mu.
Ya yi nuni da cewa, “Rundunar, karkashin jagorancin Dakta Ahmed Abodunrin, ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen yakar satar mai, da hada-hadar man fetur da duk wasu ayyukan haramtattun man fetur a jihar.
Comments 1