By Abbas Yakubu Yaura
Masu garkuwa da mutanen sun sako malamin jami’ar kimiyya da fasaha ta Kano (KUST) Wudil, Farfesa Huzaifa Karfi wanda suka rike shi bayan ya kai kudin fansa.
Matasan Gombe Sun Gudanar Da Tattakin Nuna Goyon Baya Ga Gwamna Yahya Bello
An saki Karfi ne da yammacin ranar Asabar, inda aka yi garkuwa da shi a Zariya ranar Laraba a lokacin da ya je kai kudin fansa don a sako Dagacin Karfi da ke karamar hukumar Takai a Kano, Abdulyahyah Ilu, wanda daga nan ya samu ‘yanci.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito a baya cewa wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki kauyen Karfi da ke karamar hukumar Takai a jihar Kano inda suka kashe mutum shida tare da yin garkuwa da basaraken mai shekaru 53.
An ce ‘yan bindigar sun kai farmaki kauyen ne a kan babura uku daga jihar Bauchi ta dajin Ringim da ke Jigawa.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, wakilinmu ya samu labarin cewa malamin da aka saki tare da wasu na kan hanyarsu ta komawa Kano.
A ranar Juma’a ne dai masu garkuwar suka sako Dagacin garin Karfi da ke karamar hukumar Takai mai suna Abdul Yahya Ilo bayan biyan kudin fansa da ba’a bayyana adadin suba.
Ilo wanda yanzu haka yana kwance a Asibiti yana karbar magani.