By Abbas Yakubu Yaura
Jam’iyyar Accord Party a Jihar Osun ta yi Allah-wadai da harin da aka kai a ranar Litinin da ta gabata kan ‘yan jarida da ke aikin yada labaran kamfen din Gwamnan Jihar Osun, Adegboyega Oyetola da wasu mazauna jihar da ba su ji ba ba su gani ba a garin Gbongan.
Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito an kai harin ne a yayin yakin neman zaben gwamnan jihar Osun da ke karamar hukumar Ayedaade a wani bangare na gangamin yakin neman gwamna na jam’iyyar APC ta jihar da za a yi a ranar 16 ga watan Yuli.
Haka kuma ‘yan ta’addan sun kai hari kan motar kungiyar ‘yan jarida ta kasa (NUJ) a Osun.
A cikin wata sanarwa da kungiyar yada labarai ta Accord Party ta fitar, jam’iyyar ta nuna takaici kan matakin da ta bayyana a matsayin na dabbanci tare da yin kira da a gaggauta cafke wadanda suka aikata wannan aika-aika.
A cewar sanarwar, “Mun yin Allah wadai da wannan harin da aka kai wa ‘yan jarida da sauran mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, suna gudanar da ayyukansu na yau da kullum. Yakamata a tsare wadanda suka aikata wannan aika-aika da masu daukar nauyinsu, a kuma sanya su fuskanci fushin doka.
“Tabbas mun san cewa magoya bayan jam’iyyar APC da PDP sun dade suna nuna karfinsu, don haka ya kamata jami’an tsaro su leka cikin jam’iyyun siyasar biyu.”
Jam’iyyar ta ce shirin maharan shi ne sanya jama’a cikin fargaba da kuma tsoratar da su daga fitowa su kada kuri’unsu ta yadda za a bai wa ‘yan takara masu karamin karfi rinjaye.
Jam’iyyar ta jajantawa ‘yan jaridan da suka jikkata ta kuma yi kira ga al’ummar kasar da su sauya sheka daga jam’iyyun siyasar da suka gaza dasu koma jam’iyyar Accord Party.