Rikici ya barke a jam’iyyar APC biyo bayan sanar da shugaban majalisar dattawa Ahmed Lawan a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyar, da Shugaban APC na kasa Sanata Abdullahi Adamu ya yi.
Adamu ya bayyana hakan ne a taron kwamitin zastaswa na Kasa na jam’iyar yayi a ranar Litinin a Abuja.
Sauran ‘yan takarar da suka hada da Asiwaju Bola Tinubu; Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo; Dokta Kayode Fayemi da David Umahi da dai sauransu za a ba su damar tsayawa takara a babban taron da za a yi gobe a dandalin Eagle Square, Abuja.
A wnai labari Kuma na daban…….
Shugaban kasa Muhammadu Buhari na ganawa da gwamnonin jam’iyyar APC daga yankin arewa a fadar shugaban kasa dake Abuja.
Taron na zuwa ne kwana guda gabanin babban taron jam’iyyar APC na zaben dan takarar shugaban kasa a zaben 2023 mai zuwa.
Duk da cewa shugaba Buhari ya ci gaba da rike kudurinsa na ganin an cimma matsaya, amma ba a yi wata ganawa ta fahimtar juna tsakanin ‘yan takarar shugaban kasa 23 ba.
Ganawar da Gwamnonin APC na Arewa shi ne karo na hudu a cikin shirin hadin gwiwa na Buhari na ganin jam’iyyar ta gabatar da ‘yan takarar da suka amince da shi domin a rage takun-saka da ka iya tasowa a karshen taron.
Gwamnonin da suka halarci taron sun hada da shugaban kungiyar gwamnonin APC kuma gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, shugaban kungiyar gwamnonin Arewa kuma gwamnan jihar Filato, Simeon Lalong, Abubakar Baduru (Jigawa) da Babagana Zulum (Borno).
Sauran sun hada da Aminu Bello Masari (Katsina), Abdullahi Sule (Nasarawa), Bello Matawale (Zamfara), Malam Nasir el-Rufai (Kaduna), Abdullahi Ganduje (Kano), Yahaya Inuwa (Gombe), Abubakar Bello (Niger), Jihar Yobe, Gwamna, Mai Mala Buni da Abdullrahman Abdulrazak (Kwara).