Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar wazirin Adamawa ya ce inaganta harkokin ilimi da samar da kayan karatu na zamani yana cikin kudurorinsa da zai tabbatar a kasar nan idan ya zama shugaban kasa.
Atiku a cikin wata sanarwa da ya aikewa jaridar DIMOKURADIYYA ranar Talatar nan ya bayyana fannin ilimi a matsayin daya daga cikin muhimman abubuwan da zai cimma.
KARANTA KUMA Rantsar Da Ademola Alamace Ta Haska Kasar Nan Daga Cikin Duhun Rashin Shugabanci — AA
Wazirin na Adamawa ya ce samar da kayan karatu na zamani a manya da kananan makarantu zai taimaka wajen kasar ta samu fifiko a tsakanin kasashen nahiyar Afrika.
Ya ce “Inganta harkar ilimi da kuma samar da kayan karatu na zamani a cikin manya da kananan makarantumu zai taimka wajen mayar da kasarmu Najeriya ta zama abar koyi a nahiyar Afrika.”
Ya ce da ilimi ne kawai makarantu a kasar nan zasu zama ababen koyi kamar yadda ake tura yan Najeriya kasashen waje karatu.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce idan aka inganta fannin ilimi da kayan karatu na zamani a makarantu zai mayar da Najeriya ta zama abun koyi a cikin nahiyar nan.
A Wani Labarin Kuma Gwamnatin Zamfara Ta Gargadi Jam’iyyar PDP Akan ‘Yan Bangar Siyasa
Gwamnatin jihar Zamfara ta gargadi jam’iyyar hamayya ta PDP da kar ta sa ‘yan bangar siyasa a matsayin dabarun da za ta bi domin ganin ta ci zabe a jihar.
A zantawarsa da manema labarai mataimakin gwamnan jihar, Sanata Mohammed Nasiha, a gidan gwamnatin Gusau, ya zargi jam’iyyar PDP da kuma dan takararta na gwamna da yin amfani da ‘yan barandan siyasa wajen kaddamar da hare-hare kan allunan talla da kadarori na ‘yan jihar da ba su ji ba ba su gani ba.