A yau ne ake gurfanar da jami’in dan sanda da ake zargi da laifin kisan ganganci ga bakin fata, Gerorge Floyd a gaban kotu, batu da ya janyo zanga zanga a sassan duniya.
Gidan Rediyon Jamus ya labarto cewa; a yanzu haka dai kasashen duniya sun bi sawu a wannan gangami na adawa da zalunci da cin zarafin mutane masu launi da jami’an tsaro ke ci gaba da yi, batun da ya zama gagarumi cikin abin da ake tattaunawa a Amurkar.
A ranar 25 ga watan Mayun da ya gabata ne dai George Floyd ya ce ga garinku, biyo bayan danne wuyarasa da gwiwa da jami’in dan sanda Derek Chauvin ya yi na kusan mintuna tara, har sai da ya daina numfashi.
A yau ne dai wannan dan sanda da ake zargi da laifin kisan ganganci, ke gurfana a gaban kotu.