Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika da sunan mai shari’a Monica Dongban-Mensem, mukaddashiyar shugabar kotun daukaka kara ta Nijeriya zuwa majalisar Dattawan Nijeriya domin tabbatar da ita a matsayin shugabar kotun.
Kakakin shugaban kasar, Malam Garba Shehu, shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja a ranar Litinin.
Sanarwar ta ce kamar yadda yake bisa ka’ida hukumar shari’a ta kasa ce ta aika da sunanta ga shugaban kasa, inda kuma shugaban kasar ya zabi Mai Shari’a Dongban-Mensem a matsayin wacce za a nada a matsayin shugabar kotun.
A ranar 29 ga watan Mayu ne, shugaba Buhari ya tsawaita wa’adin mai shari’a Dongban-Mensem a matsayin shugabar kotun.
Tsawaita wa’adin zai fara aiki ne daga 3 ga watan Yuni har zuwa tsawon wata uku.