Rundunar ‘yan sandan Nijeriya reshen Delta, ta cafke Fasto din da ake zargi da yiwa ‘yar shekara 19 fyade. Wacce aka yiwa fyaden memba ce a Cocin Faston da ake zargi a garin Warri.
Kwamandan ‘yan sandan yankin, Mohammed Garba shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Litinin a Warri.
A cewar Garba, wanda ake zargin mai suna Bishop Elijah Orhonigbe, shi ne jagoran Cocin Victory Revival Fasting and Prayer Ministry dake Warri.
Ya kuma tabbatar da cewa an cafke shi ne a ranar 5 ga watan Yuni, kuma tun lokacin ake ci gaba da rike shi a ofishin ‘yan sandan. Ya ce an cafke shi ne bayan karar da mahaifiyar wacce aka yiwa fyade ta shigar.