Shugaban babbar jami’iyyar adawa a Tanzania, Freeman Mbowe yana kwance a asbiti bayan afka masa da wasu da ake zargin mahara da ba a san ko su wane ne ba suka kai masa.
Wata sanarwa daga ofishin ‘yan sandan yankin ta bayyana cewa labari ya riske su ne inda aka bayyana musu cewa; wasu mutane uku ne suka afkawa Mbowe din har sai da suka karya mai kafarsa ta dama, lamarin da ya sanya aka kwantar da shi.
Jam’iyyarsa ta Chadema ta tabbatar da labarin, inda suka wallafa a shafin Twitter cewa Mbowe yana kan hanyarsa ta komawa gida ne ya gamu da wadannan bata gari da suka yi mai wannan ta’adi.