Wani masanin tattalin arziki, Dokta Ayo Anthony ya ce sabuwar manufar kudi da Gwamnatin Tarayya ta yi na iya taimakawa wajen rage hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya cikin dogon lokaci.
Anthony ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Lahadi a Abuja.
Ya yi magana game da yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi bayani na kasa a ranar Alhamis.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tuna cewa shugaban kasar a cikin sakonsa na kalubalen musanya kudi da kuma halin da kasar ke ciki, ya ce daya daga cikin abubuwan da manufar kudin za ta cimma a takaice da matsakaita da kuma dogon zango, shi ne rage hauhawar farashin kayayyaki.
KU KARANTA KUMA Hanyar Magance Mtsalar Hauhawar Farashin Kayan Abinci
A cewar shugaban, a cikin gajeren wa’adi da matsakaici da kuma dogon zango, ana sa ran za a samu raguwar hauhawar farashin kayayyaki a sakamakon raguwar kudaden da ake samu tare da rage saurin hauhawar farashin kayayyaki.
Masanin tattalin arzikin, ya ce a cikin gajeren lokaci da tsakiyar lokaci, manufar ba za ta iya rage yawan hauhawar farashin kayayyaki ba.
A cewarsa, a nan gaba, manufar za ta iya yin aiki kuma za ta iya taimakawa wajen rage hauhawar farashin kayayyaki ita kuma hauhawar farashin kaya a Najeriya lamari ne na kudi.
“Misali, bisa kididdigar da aka fitar, CBN ya ce kusan Naira Tiriliyan 3 ne kudin da ke yawo a kasuwannin duniya, abin da ka kira tsabar kudi a ke bayarwa kenan.
“Amma daga cikin abin da ake kira Naira Tiriliyan 3 da ke yawo, fiye da kashi 60 cikin 100 na sa ba ya yawo kuma har yanzu farashin kaya yana karuwa.
“Fiye da kashi 60 cikin 100 na wannan kudi ba sa bukatar hakan wanda ke nufin ba a bangaren banki ba ne.
“Idan kudi ke haifar da bukatar, za ku iya cewa kudi ne sanadin hauhawar farashin kayayyaki.”
Anthony, don haka ya ce hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ba batun wuce gona da iri ba ne wajen samar da kayayyaki.
A Wani Labarin Kuma PSC Ta Nada Ko’odinetoci Domin Sa Ido Kan Halin Jami’an ‘Yan Sanda A Lokacin Zabe
A yayin da al’ummar kasar ke kidayar lokacin babban zabe na 2023, hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda, hukumar zartaswa ta tarayya da tsarin mulki ya bada ikon ladabtar da jami’an ‘yan sanda in ban da sufeto Janar na ‘yan sanda, da sauran ayyuka, sun nada ko’odinetocin kasa, shiyya-shiyya da na Jiha domin gudanar da wannan atisayen. Tuni dai hukumar ta amince da halartar sama da ma’aikatanta 360 da za su tashi zuwa jihohin kasar nan 36 domin sanya ido kan yadda ‘yan sanda ke gudanar da ayyukan zabe.
Hukumar ta yi gargadin cewa za ta sanya takunkumi ga duk wani dan sandan da ke da hannu a duk wani nau’i na rashin da’a kafin lokacin zabe ko kuma bayan zaben kamar yadda ta kuduri aniyar tabbatar da cewa ‘yan sandan da ke aikin zabe dole ne su gudanar da aikinsu bisa ka’idojin da aka amince da su.