Shugaban Kasar Senegal Macky Sall ya killace kansa biyo bayan wata ganawa da yayi da wani mutum da aka gano yana dauke da cutar sarƙe numfashi.
Kamuwar mutumin da cutar ta bayya ne bayan ganawarsa da Mista Sall a cewar Fadar Shugaban Kasar.
Gwamantin ƙasar Senegal ta ce Shugaba Sall zai ci gaba da kasancewa a killace na tsawon mako biyu domin tabbatar da lafiyarsa.
Sanarwar da ofishin shugaban kasar ya fitar ta ce gwajin da aka yi, ya nuna cewa shugaban kasar bai harbu da kwayar cutar ba, amma zai ci gaba da killace kansa a matsayin riga-kafi.
Fadar gwamnatin ƙasar ta yi kira ga ‘yan kasar da su kwantar da hankalinsu tare da bin matakan kariya daga cutar.
Har wa yau, sauran hadiman fadar gwamnatin su ma an shawarce su da su killace kansu domin rigakafi ga lafiyarsu.