Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Larabar nan, a wajen taron majalisar zartarwa ta tarayya, FEC ya yabawa ministocinsa bisa biyayyar da suka nuna tun 2015.
Buhari ya kuma ce kammala mulkin Najeriya, tamkar dama ce gare shi domin kuwa zai samu lokacin kula da shanunsa a mahaifarsa ta Daura, jihar Katsina.
KU KARANTA: Ku Ci Gaba Da Zama A Ofisoshin Ku Har Zuwa 29 May – Sakon Buhari Ga Ministocin sa
Shugaban ya kuma yabawa ma’aikatan fadar gwamnatin jihar bisa goyon bayan da suka bayar a gwamnatinsa na tsawon shekaru takwas.
A jawabinsa a wajen taron bankwana da aka gudanar a zauren majalisar da ke fadar shugaban kasa a Abuja, shugaban ya gode wa dukkan ministocin bisa jajircewar da suka nuna wajen ganin an cimma manufofin gwamnatin.
Ya kuma bukaci goyon bayan shugaban kasa mai jiran gado, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, wajen ɗorawa kan muhimman ayyukan raya kasa da ya fara.
Ya yaba wa ministocin saboda yin aiki kafada da kafada, duk da matsaloli da kalubale da dama, da kuma dorewar hadin gwiwa da ke bayuwa kai tsaye zuwa ga nasarori da dama.
DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa Shugaban ya umurci ministocin da su ci gaba da gudanar da ayyukansu tare da kaucewa gaggawar da ka iya kawo cikas ga ayyukan alheri da suka yi tsawon shekaru.
Shugaba Buhari ya danganta dukkan ayyukan alheri da fatan alheri da gwamnatin ta samu da cewa Allah ne ya nufi hakan.
A wani labarin kuma: Ministan Buhari Ya Caccake Shi Gabanin Sallama Da Mulki
Karamin Ministan Kwadago da nagartar ayyuka mai barin gado Festus Keyamo, SAN, ya shaidawa shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa hadin rigima ne a nada karamin minista.
Keyamo ya bayyana haka ne a jawabin da ya gabatar a wajen taron karramawar da shugaba Buhari ya jagoranta na bikin karshen majalisar zartarwa ta tarayya FEC a karkashin gwamnatin shugaba Buhari a Larabar nan.