Ƙungiyar kare hakkin ɗan-Adam ta ƙasa da ƙasa, Amnesty International ta ce ’yan bindiga sun kashe aƙalla mutum 1,126 a ƙauyukan dake Arewacin Najeriya cikin watanni shidan farkon wannan shekara.
Ta ce kashe-kashen sun faru ne a jihohin Kaduna, Katsina, Neja, Filato, Sokoto, Taraba da kuma Zamfara, tare da zargin sojojin Najeriya da gaza kare su a yayin da hare-haren ƙungiyar Boko Haram ke ƙaruwa.
A sanarwa da ta fitar ranar Lahadi, Amnesty ta zargi mahukunta da rura wutar kashe-kashe da satar jama’a saboda gaza gurfanarwa da kuma hukunta masu aikata laifukan.
Ta kuma ce tana da cikakkun rahotannin cin zarafin manoma da ƙungiyoyin kare hakkin ɗan-Adam da ke yin kira ga gwamnati ta ɗauki matakan da suka dace.
“Rashin yin katabus daga jami’an tsaro wajen kare rayukan jama’a daga waɗannan hare-hare abun kunya ne matuka,” inji Daraktan Anmnesty a Najeriya, Osai Ojigho.
“Bugu da ƙari, jami’an tsaro na jan kafa wajen kai ɗauki ga jama’a bayan samun gargaɗi ko barazana daga mahara da kuma rashin hukunta waɗanda aka kama ya sa ’yan ƙauyukan sun rasa madafa”, inji ta.
Ƙungiyar ta yi zargin cewa yawanci maharan a kan babura ɗauke da muggan makamai kan yi wa ƙauyukan ƙawanya suna harbi kan mai uwa da wabi, su ƙona gidaje wuta, su sace dabbobi da amfanin gona da kuma mutane domin neman kuɗin fansa.
Ta ce aƙalla mutum 380 aka sace a jihohin Kaduna, Neja, Katsina, Nasarawa da Zamfara a 2020, yawancinsu mata da ƙananan yara.
Har wa yau, ’yan bindigar kan kashe iyalan da suka gaza biyan kuɗaɗen fansar da aka yanka musu.
Amnesty ta ce akwai wani hari da aka kai Unguwar Magaji a Jihar Kaduna amma ko da jami’an tsaro suka je wajen, da suka ga makaman maharan sun fi nasu sai suka juya, kafin su dawo kuma an kashe kusan mutum 17.
A Jihar Taraba kuwa, ƙungiyar ta ce aƙalla mutum 77 rikicin ƙabilanci tsakanin ƙabilun Tibi da Jukun ya hallaka.
A ranar 28 ga watan Mayu kaɗai, a cewar, harin ’yan bindiga ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 74 a ƙaramar hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoto
A Katsina, rikicin ya yi sanadiyyar raba manoma da dama da gonakinsu da kuma iyalansu.
Kimanin mutum 33,130 ne a waɗannan jihohin yanzu suke zaune a sansanonin gudun hijira. Wasu kuma sun koma wurin ’yan uwa, yayin da dubban manoma kuma a bana ba za su iya noma gonakinsu ba.
Ƙungiyar ta yi kira ga mahukuntan Najeriya da su tashi tsaye wajen gudanar da bincike a kan kashe-kashen tare da hukunta waɗanda duk aka samu da laifi.
To sai dai da aka tuntuɓe shi a kan rahoton na Amnesty, Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Najeriya, Frank Mba bai cw komai ba game da lamarin.
Wannan ba shi ne karon farko da rahoton ƙungiyar ke zargi hukumomin Najeriya da gaza kare rayuka da dukiyoyin jama’a yayin waɗannan hare-haren ba.