Sabbin alkaluman hukumar daƙile cutuka masu yaduwa a Nijeriya, NCDC, sun nuna cewa mutum 44 kawai aka samu dauke da korona a faɗin ƙasar a jiya Litinin.
Jihohin da aka samu masu dauke da cutar sun hada da Enugu mai mutum 22 da Legas mutum 15 sai kuma Abuja mutum 4.
Akwai kuma jihar Osun mai mutum 2, da mutum guda a Kaduna.