Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bukaci kasar Afrika ta Kudu ta kare rayuka da dukiyar ‘yan kasashe da dama da ke zaune a kasarta sakamakon cin zarafin da suke fuskanta musamman a birnin kasar Johannesburg.
Shugaba Buhari ya bukaci hakan ne a yayin wata doguwar tattaunawa da ya yi da shugaban kasar Cyril Ramaphosa kan yadda za a bunkasa tattalin arzikin kasashen biyu a ranar Alhamis.
Ana dai sa ran tattaunawar ta su za ta kawo karshen cin zarafi da tada rikice-rikicen da ake yi a yankunan da ‘yan kasashe da dama ke zaune a kasar musamman ma ‘yan Nijeriya da suka sha fuskantar matsaloli.
Rahotonni sun bayyana cewa, ko a watan Satumban da ya gabata an balle wasu manyan shagunan kayan masarufi tare da yi musu sata da kuma banka musu wuta a Johannesburg, wanda kuma dukkan su mallakin ‘yan kasashen ketare ne daban-daban ciki kuwa har da na ‘yan Nijeriya.
Ko a kwanakin baya rikicin kasar ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutum 12 baya ga daruruwan mutane da suka yi gudun hijira sanadiyyar rikicin.
A na shi jawabin, shugaba Cyril Ramaphosa na Afrika ta Kudu, ya nanata bada hakuri bisa hare-haren, tare da bayyana rashin jin dadinsa kan ayyukan ta’addancin da ya auku a kasar yana mai cewa gwamnatinsa ta yi nadamar faruwar hakan.