Tsohon dan wasan Arsenal da Chelsea da Barcelona, Cesc Fabregas ya bayyana masu horas da ‘yan wasa biyu da ba shi da kamar su.
Cesc Fabregas ya ambaci Arsene Wenger da Jose Mourinho a matsayin manyan manajoji guda biyu da ya yi aiki a karkashinsu a lokacin da yake taka rawar gani.
Dan wasan na Monaco a yanzu ya taba taka leda a Arsenal, Barcelona, Chelsea inda ya ci kofi uku.
Sannan yana takawa kasarsa ta Sipaniya.
A shekarar 2010, Fabregas ya dauki Kofin Duniya. Da kuma kofin Yuro a 2008 da 2012.