Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da shirin ci gaba da rufe kan iyakokin kasar har gaba da ranar 31 ga watan Janairun shekara mai zuwa.
Babban Jami’in Hukumar Kwastam da ke Kula da sashen bincike da kuma sa ido, David Dimka ya sanar da haka a wasikar da ya rubuta wa jami’an hukumar da ke jihohi da kuma kan iyakokin kasar.
Rufe iyakokin na zuwa ne watanni uku kacal bayan Nijeriya ta sanya hannu kan yarjejeniyar kasuwancin bai daya tsakanin kasashen Afirka.
Matakin rufe kan iyakokin na ci gaba da haddasa cece-kuce, inda wasu ke lale marhabin da shi, yayin da wasu ke kokawa saboda a ganinsu, matakin shi ne ummul-haba’isin tashin farashin kayayyaki a kasuwannin Nijeriya da suka hada da abinci.