Daga: Wakilin Dimukaradiyya Mukhtar Yakubu
Sabuwar jaruma a Masana’antar shirya fina-finai ta Kannywwod Nadiya Adamu wadda ta zo Kano daga Kasar Nijar ta bayyana mamakin ta da halayyar wasu daga cikin masu gudanar da harkar su a cikin Masana’antar musamman a Kan Sabuwar fuska data shigo cikin su.
Jarumar ta bayyana Hakan ne a lokacin tattaunawar su da Jaridar Dimukaradiyya in da take bayyana cewa.
“Tun Ina karama na ke sha’awar shiga shirin fim saboda yawan kallon fina-finan Hausa dana ke yi Musamman wakoki, wannan ce ta sa dana girma sai na taho daga Kasar mu Nijar don na shiga harkar.
Jarumar ta ci gaba da cewar” To Alhamdulillahi yanzu Burina ya cika na zo Kuma ga shi Ina yin fim din har an fara sani na a yanzu idan na je wani waje sai ka ga ana kallona ana sha’awa ta, gaskiya abin ya na burge ni.”
A game da yadda ta samu kanta a Masana’antar kuwa a matsayin ta na Sabuwar jaruma cewa ta yi.
“To gaskiya a cikin harkar fim akwai mutane masu kirki wadanda in za su yi maka abu sai su yi maka don Allah. Amma akwai wasu Kuma in dai za su yi maka wani abu za su ce sai ka ba su kudi ko Kuma su ce sai ka ba su wani abu. Don haka a cikin harkar fim, akwai masu kirki, akwai Kuma wadanda halin su ba na kirki ba ne. “
Daga karshe ta yi Kira ga abokan sana’ar ta da cewar ya kamata in za su yi abu su rinka yin sa don Allah, musamman wadanda su ke ganin sai an ba su wani abu za su yi wa mutum abin da ya ke so.
Comments 1