Prince Walson, wanda aka fi sani da Mr. Sab, mawaƙin Afrobeats kuma marubuci, ya bayyana cewa ba zai hana ‘ya’yansa ko kawo musu cikas ba idan suka zaɓi yin sana’ar waƙa, Tribune Online ta rawaito.
“Waƙa tana bunƙasa a cikin iyalina, kuma ba zan yi mamaki ba idan dukan ’ya’yana sun soma sha’awar kiɗa,” in ji shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Dumi-Dumi: Dan Gwamnan Jihar Nasarawa Ya Rasu
Mawakin ya kuma ambata cewa ya sami damar yin kida da kuma samun lokaci ga iyalinsa.
Mawakin ya kuma ce duk da cewa sana’arsa ta waka ba ta samu sauki ba, amma ya iya daurewa lokacin da komai ya ci tura saboda jajircewarsa da sha’awar aikin.
“Sha’awar kiɗa da sauran ƙoƙarce-ƙoƙarce na nishaɗi koyaushe yana da ƙarfi. Baya ga kiɗa, ni ɗan kasuwa ne wanda ya san cewa kasancewa mai dacewa yana buƙatar ci gaba mai kyau.”
“Babu wani abu da zai iya raya wannan alamar in ba tare da kasancewar Allah a rayuwata ba, don haka ina godiya ga rahamar Allah a gare ni.”
A wani labarin kuma, An Tsaurara Matakan Tsaro Yayin Da Kotu Ke Yanke Hukuncin Zaben Gwamnan Osun
A wani labarin kuma, A yayin da kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Osun ke yanke hukunci a yau, an tsaurara jami’an tsaro da dama a harabar babbar kotun da ke Osogbo da kewaye.
Tsohon gwamna Adegboyega Oyetola ya kalubalanci sakamakon zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 16 ga watan Yuli inda ya ce an tafka kura-kurai tare da nuna shakku kan cancantar Gwamna Ademola Adeleke na tsayawa takarar zaben.