Bangaren Sanata Kabiru Marafa na jam’iyyar APC a jihar Zamfara, ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta daina yin siyasa da harkokin tsaro da addini domin amfanin jihar da kasa baki daya.
APC ta ce dora rashin tsaro da addini domin amfanin siyasa zai fi illa ga jihar fiye da alheri
A wata sanarwa da mai magana da yawun kungiyar Marafa ta APC Bello Bakyasuwa Maradun ya sanyawa hannu, ta ce a baya-bayan nan abin da ya faru a Zamfara inda yakin cacar baki tsakanin gwamnatin jihar da babbar jam’iyyar adawa ta PDP yake kamari, kuma wani ci gaba ne da ya kamata a shawo kan lamarin kafin ya bar hannun.
“A cikin ‘yan kwanakin nan, kowane mako yana zuwa da wata cece-kuce ko kuma wani daga gwamnatin jihar inda ake zargin manyan ‘yan siyasa na adawa da wani kamfen na yaudara da addini da rashin tsaro” Bakyaswa ya ce.
Bangaren Marafa ya kuma nisanta kansa daga wani labari da aka wallafa cewa an kama wani da ake zargi sanye da riga mai dauke da hoton Sanata Kabiru Marafa a yayin wani farmaki da sojoji suka kai wa ‘yan bindiga.
Sun bayyana labarin a matsayin mara tushe balle makama. Bangaren APC ya kuma fusata kan zargin da ake yi wa Muttaka Rini da Dauda Lawal Dare wadanda ke cikin bangaren tsohon Gwamna Yari.
Bangaren Marafa na APC ya ce yunkurin wayar da kan al’umma kan wasu al’amura da ke tasowa a Zamfara ba wai don Allah-wadai da Gwamnatin Gwamna Bello Matawalle ba ne, sai dai a hada kai wajen gyara al’amura.
“Niyyarmu ita ce alheri ta yadda za a iya sanya hannun jarin mu don gina jiharmu da muke kauna”
“Mun kuma kudure aniyar hada kai wajen yakar abokan gaba na rashin tsaro da ‘yan bindiga ke haddasawa da kuma taimaka wa dubban daruruwan ‘yan gudun hijira a cikin jihar” Bakyaswa ya tabbatar.
Comments 1